1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Buhari ya fara ziyarar aiki Landan

Abdoulaye Mamane Amadou
July 26, 2021

Shugaba Muhamadu Buhari na Najeriya zai fara wata ziyarar aiki ta makonni biyu a birnin Landan na Birtaniya, inda zai halarci taron kolin kasa da kasa da aka shirya kan ilimi.

https://p.dw.com/p/3y5lZ
Krise in Mali | ECOWAS | Muhammadu Buhari
Hoto: Présidence du Mali

Sai dai ko baya ga taron kolin kan ilimi, Shugaba Buhari mai shekaru 78 a duniya zai gana da likitansa domin duba lafiyarsa kamar yadda wata sanarwa ta fadar shugaban kasar ta bayyana.

Tun a karshen watan Yunin da ya gabata ne dai ya kamata shugaban ya ziyarci likitansa, to amma aka dage tafiyar ba tare da bayar da wasu cikakkun hujjojin da suka hana hakan ba daga fadar shugaban kasar.

Fitar shugaban zuwa Landan don ganin likita na haifar da zazzafar mahawar a kasar mafi yawan al'umma a nahiyar Afirka, musamman ma kan batun ingancin yanayin kula da lafiyar al'umma.