1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru biyar da kisan Khashoggi

Yaya Azare Mahamud
October 2, 2023

Shekaru biyar bayan kisan gillar da aka yi wa Jamal Khashoggi dan jaridan nan dan Saudiyya, kungiyoyin kare hakkin dan Adam na ci gaba da lasar takobin ganin anbi kadi.

https://p.dw.com/p/4X3FG
Turkiya, birnin Santanbul | Jamal Khashoggi dan jarida na Saudiyya da aka halaka
Tunawa da Marigayi Jamal KhashoggiHoto: picture-alliance/AP Photo/L. Pitarakis

Kitsa kisan gillar da jami'an tsaron Saudiya sukaiwa dan jaridar Jamal Khashoggi, da kewa masarautar ta Saudiya sukar gyara kayankan da bai taba zuwa sauke mu raba ba, shi ne mafi muni da aka taba yi wa wani dan jarida a kasashen Larabawa da ya jijjiga duniya, a rana irin ta yau, wato ranar biyu ga watan Oktobar shekarar 2017, yadda bayan shake shi har ya mutu, aka yi gunduwa-gunduwa da gaggan jikinsa, kafin a narkar da ita ta bace bat.

Shi kansa Muhammad Bin Salman da jami'an liken asirin Amirka suka tabbatar da cewa, shi ya ba da umarni kai tsaye na share Jamal Khashoggi daga doron kasa, ya siffanta kisan da akai masa da kisa mafi muni da ke ta da tsikar jiki:

Amirka | Zanga-zanga kan mahukuntan Saudiyya | Jamal Khashoggi
Zanga-zanga kan mahukuntan Saudiyya bisa kisan Jamal KhashoggiHoto: JIM WATSON/AFP/Getty Images

Matsin lambar kafofin watsa labarai da kasashen duniya,musammama kasar Turkiyya da akai kisan a cikinta, ya tilastawa mahukuntan na Saudiya amsa laifinsu kan cewa su sukai kisan amma bisa kuskure, yadda akai hukuncin jeka na yi ka da mutane 9 daga cikin 22 da aka yi ammanar sun kitsa yi wa dan jaridan kisan sun kuma cika.

Hakan dai bai sanya kasar ta Saudiyya ta iya wanke kanta ba, yadda jagoranta, yarima mai jiran gadon mulki da bincike mai zaman kansa na Majalisar Dinkin Duniya ya tabbatar da hanunsa dumu-dumu kan kisan, ya zama saniyar ware a duniya. To sai dai a yanzu, shekaru biyar da wannan mummunar aika-aika, an yi juyin dan waken zagaye, yadda kusan duniya ke neman mantawa da wannan kisan, yayin da Bin salman ya dawo ana damawa da shi dumu-dumu cikin lamuran siyasa da tattalin arzikin duniya.

Bayan kisan Khashoggi dai, kungiyar fafutukar girka dimukiradiyya a Saudiyya da ke da ofishinta a BIrtaniya, ta ce baya ga kisan Khashoggi, har yanzu, 'yan ina da kisan masarautar ta Saudiyya, na ci gaba da farautar 'yan adawa na Saudiyya, kamar yadda kungiyar 'yan jarida ta kasashen Larabawa ta yada wani jawabin da Khashoggi ya taba yi kan hakkin fadin albarkacin baki inda ya soki hukumomin.