1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta zauna a rabe bayan yakin duniya na biyu

October 7, 2019

Litinin 7 ga watan Oktoban 2019 aka cika shekaru 70 da kafa tsohuwar kasar Jamus ta Gabas da ta kasance karkashin tsarin Kwaminisanci. Bayan yakin duniya na biyu Jamus ta zauna a rabe.

https://p.dw.com/p/3Qq4x
Berlin | DDR vor 70 Jahren gegründet - Archivbild vom 07.10.1989
Hoto: picture-alliance/dpa

Jamhuriyar Dimukuradiyyar Jamus ko Jamus ta Gabas wannan shi ne sunan kasa ta biyu ta Jamus da aka kafa cikin watan Oktoban shekarar 1949 shekaru hudu bayan kawo karshen yakin duniya na biyu, kuma watanni hudu bayan kafuwar daya kasar ta Jamus wato Jamhuriyar Tarayyar Jamus ko Jamus ta Yamma. Raba kasashen Jamusawa ya dace da tsarin da kasashen Amirka da Birtaniya da Faransa da kuma Tarayyar Sobiet suka yi ne bayan sun murkushe gwamnatin 'yan Nazin Jamus. Yayin da Jamus ta Yamma ta kafa tsarin dimukuradiyya irin na yammacin duniya ita ko Jamus ta Gabas ta bi tsarin kwaminisancin har izuwa lokacin da aka samu sauyi a shekarar 1989 zuwa 1990 a kasashe irinsu Poland da Hungary da Romaniya da kuma ita kanta Jamus ta Gabas.

Karte Deutschland vor der Wiedervereinigung HA

A tsakanin kasashen yankin gabaci dai JTG ta kasance abu na musamman saboda kan iyakarta ta yamma yankin Turai mai 'yancin walwala ya fara, a kuma tsakiyar birnin Berlin da wata katanga da aka kammala aikinta a shekarar 1961 ta raba gida biyu. Saboda haka ne ma yammacin Berlin ya zama wani tsibiri na 'yanci a tsakiyar gabacin Jamus mai bin tsarin kwaminisanci har zuwa ranar 7 ga watan Oktoban 1989 lokacin da gwamnatin Jamus ta Gabas ta yi bikin cika shekaru 40, wanda kuma shi ne na karshe a matsayin kasa ta kwaminis. Sannan a ranar 9 ga watan Nuwamban 1989 katangar Berlin ta fadi, sannan shekara guda baya wato ranar 3 ga watan Oktoban 1990 aka sake hade kasashen Jamusawan biyu.