1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Sharhunan Jaridun Jamus: 08.12.2023

Usman Shehu Usman AH
December 8, 2023

Batutuwan harin soji a Najeriya kan farar hula da sabuwar yarjejeniya tsakanin Rasha da Nijar, da yunkurin juyin mulki a Saliyo da Guinea Bissau sune suka dauki hankali a Jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/4ZwQH
Jemen Drohne Modell
Hoto: picture alliance / Anadolu

Jaridar Der Tagesspiegel, ta ce wani hari da jiragen yaki marar matuki suka kai kan masu yin bikin Mauludi a Najeriya, ya kashe fararen hula akalla 85. Hukumar kula da bala'o'i ta ce an riga an yi jana'izar mutane 85 da suka mutu, bayan harin da aka kai a wani kauye da ke Jihar Kaduna a arewa maso yammacin kasar. A yanzu dai jaridar ta ce ana ci gaba da jinyar karin mutane wadanda abin ya shafa. Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan lamarin.

Sabon kawance Njiar da Rasha babbar barazana ga Turai

Hoto: Sam Mednick/AP/dpa/picture alliance

Die Welt kuwa ta duba sabon kawancen Rasha da Nijar ne. Jaridar ta ce wai shin sabuwar kofar Moscow ne kenan? Ana dai ci gaba da yanke shawarar makomar yankin Sahel da siyasar Nijar tun bayan da kasashen yamma suka sha kaye a yakin da ake yi da ta'addanci. Ya zuwa yanzu dai, kasar ta Nijar da ke zama babbar hanyar hijirar daga Afirka izuwa Turai ta yi kasa a gwiwa kan ko za ta juya bayanta ga kungiyar tarayyar Turai ta koma bangaren Moscow. Yanzu an fara wata sabuwar yarjejeniya alama ce kuma a bayyana ne. Ba ya ga wata yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Rasha da Nijar, a hukumance kasashen biyu sun fara tuntubar juna don kwalla wani kawance mai girma, wanda kuma zai rage fada ajin Turai a Nijar. Jaridar dai na magana ne kan wata tawagar Rasha da ta kai ziyara a Jamhuriyar Nijar cikin wannan mako. Amma cewar jaridar ga wasu talakawan Nijar tuni suka rungumi kasar Rasha inda hatta a bakin shaguna ko kuma kayan tallansu kan titi suke dora tutar Rasaha a kai.

Yunkurin juyin milki a Saliyo da Guinea Bissau

Mataimakin jagoran sojojin Guinea Bissau  Mamadú Turé
Mataimakin jagoran sojojin Guinea Bissau Mamadú Turé Hoto: DW

Sai wani batun juyin mulkin a yammacin Afirka. inda jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta ce harbe-harbe a Bissau da Freetown. Jaridar ta ce shugabannin Guinea-Bissau da Saliyo duk sun yi magana game da yunkurin juyin mulki wa gwamnatocinsu. A cewar gwamnatocin kasashen biyu, an yi yunkurin juyin mulki sau biyu a yammacin Afirka cikin 'yan kwanaki. An dai fara ne da Saliyo sannan kuma a Guinea-Bissau. Kafofin yada labaran cikin gida da farko sun bayar da rahoton harbe-harbe a Bissau babban birnin kasar. Sojoji sun kubutar da ministan kudin da aka kama da kuma sakataren gwamnatin kasar daga hannun 'yan sanda. Jami'an tsaron fadar shugaban kasar sun tafi da su biyun zuwa wani wuri da ba a san ko su waye ba, sannan suka yi wa kansu shingen tsaro a barikin sojoji, kamar yadda aka ce. A lokacin wannan lamarin ke faruwa shugaban kasar ya fita wajen kasar. Kwana guda bayan yunkurin juyin mulkin Shugaba Umaro Sissoco Embaló ya dawo daga taron sauyin yanayi da aka yi a Dubai kuma ya yi magana kan yunkurin juyin mulki wa gwamnatinsa. Da tsakar rana ne sojojin suka sanar da kama kwamandan tsaron kasar tare da mika wuya, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito. Bayan haka, da alamun kwanciyar hankali ta dawo, inda ake ci gaba da ganin motocin sojoji a kan titunan babban birnin kasar. Akalla mutane biyu aka ruwaito sun mutu a yunkurin juyin mulkin.

Birtaniya za ta jingine kare hakkin bil'Adama don biyan bukatunta 

Firaministan Birtaniya Rishi Sunak
Firaministan Birtaniya Rishi Sunak Hoto: Stefan Rousseau/Pool/AP/picture alliance

Birtaniya na son yin watsi da hakkin dan Adam, da gangan a cikin yarjejeniyar 'yan gudun hijirar da ta kulla da Rwanda, wannan shi ne labarin jaridar die Zeit. Gwamnati a London ta fito fili ta yarda cewa tana son dakatar da dokar kare hakkin dan Adam saboda shirin korar baki. Firaminista Sunak, yana son tabbatar da cewa ba a dakatar da shirin ba. Rishi Sunak da jam'iyyarsa da ke kan mulki, suka ce wani sabon kudiri zai tanadi cewa ba za a iya amfani da muhimman sassa na dokar kare hakkin bil'Adama ta Birtaniya, da ke bukatar 'yancin dan Adam a shari'ar Ruwanda. Wannan zai tabbatar da "ba za a iya dakatar da shirinmu ba," wato dai Birtaniya za ta jingine kare hakkin bil'Adama don biyan bukatunta.