1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Scholz ya yi alkawarin kara taimaka wa Ukraine

Sabine Kinkartz SB
July 17, 2023

Olaf Scholz ya yi taron manema labarai na shekara-shekara gabanin fara hutun lokacin bazara, inda ya tattauna kan batutuwa da dama da suka hada yaki tsakanin Rasha da Ukraine.

https://p.dw.com/p/4TzkG
Olaf Scholz shugaban gwamnatin Jamus
Olaf Scholz shugaban gwamnatin JamusHoto: Michael Kappeler/dpa

Yakin da ke faruwa tun lokacin da Rasha ta kaddamar da kutse kan Ukraine yana cikin batutuwan da shugaban gwamnatin ta Jamus, Olaf Scholz ya mayar da hankali inda ya ce kamar yadda kasar ta yi alkawarin tana taimakon Ukraine domin kare kanta tun lokacin da yakin ya balle: "Muna taimakon Ukraine ta hanyoyin jinkai, da kudi amma kuma har da makamai domin kare kasarsu domin tabbatar da kare iyakokin kasar. Ba mu kadau muke yi ba, amma tare da kasashe kawayenmu. Baya ga Amirka, yanzu Jamus tana sahun gaba na taimakon  Ukraine, da kayan soja da makaman da suke bukata." Sannan ya kara da cewa kamar yadda Jamus ta yi alkawari da kara yawan kudin da kasar take kashewa tun lokacin da yakin ya balle tare da ware kimanin kudin Euro milyan dubu-17 kan harkokin soja na taimakon da Jamus za ta yi ga Ukraine. Scholz ya bayyana cewa daga yanzu an karfafa kashe kudin tsaron kasa ke'nan: "Mun amince da kashe kashi biyu cikin 100 na karfin tattalin arzikinmu kan tsaro na rundunar Bundeswehr. A shekara mai zuwa za a cimma wannan burin a karon farko a kasafin kudi da aka saka kudi na musamman kuma abin da zai ci gaba ke'nan bayan amfani da kudin."

Jamus ta rage yawan dogaro da China

Bundeskanzler Olaf Scholz im Bundestag
Hoto: Kay Nietfeld/dpa

Wani abin da gwamnatin ta yi shi ne tabbatar da rage dogoron kasuwancin kan kasar China wadda take zama babbar abokiyar cinikayya ta Jamus. Karkashin sabbin manufofin Jamus za ta karfafa zuba jari a sauran kasashe. Duk da yake kamfanonin Jamus sun nuna dari-dari kan sabbin manufofin.

Jam'iyyar AFD ta masu kyamar baki ba za ta yi tasiri ba a zaben gaba

Olaf Scholz shugaban gwamnatin Jamus
Olaf Scholz shugaban gwamnatin JamusHoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

Shugaban gwamnatin Olaf Scholz ya ce jami'iyyarsa ta  SPD da Greens gami da FDP da ke cikin kawancen gwamnatin suna kokarin samun matsaya kan batutuwa da dama gami da manufofin kasar. Sannan yana nuna cewa jam'iyyar AfD ta samu ra'ayin kyamar baki babu wani gagarumin tasirin da za ta yi  yayin zaben kasar da ke tafe, sannan Scholz ya ci gaba da cewa: "Ina da karfin gwiwa cewa jam'iyyar AfD ba za ta taka wata rawar a zo a gani ba lokacin zaben kasa baki daya da ke tafe. Haka na zuwa ne sakamakon yadda ake ganin kamar jam'iyyar tana kara samun tagomashi. Game da masu neman shiga kasar shugaban gwamnatin ya ce gwamnatin za ta ci gaba da bin shirye-shiryen da aka tsara wajen shigar da mutanen da suka dace, wadanda za su taka rawa a bangaren ayyuka wajen inganta tattalin arziki. Sannan ya ce za a tabbatar da ganin samun daidai tsakanin mutane da za su shigo daga nahiyoyin duniya dabam-dabam.