1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Scholz ya bukaci karin hadin kai da kasashen Afirka

Zainab Mohammed Abubakar
May 7, 2023

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz da shugaba William Ruto na Kenya sun amince da bukatar zuba jari a fannoni masu yawa a tsakanin kasashen biyu.

https://p.dw.com/p/4R0dN
Kanzler Scholz in Afrika | Kenia Geothermiewerk Olkaria
Hoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

A ranar asabar ce shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya kammala rangadin kwanaki biyu da ya kai kasashen Habasha da Kenya da ke yankin gabashin Afirka, tare da gane wa idanunsa aikin samar da makamashi mara gurbata yanayi a tafkin Naivasha a Kenya.

Tashar mai tazarar kilomita 120 daga arewa maso yammacin Nairobi na zama irinsa mafi girma a Afirka, wanda ke dauke da tashoshin wutar lantarki guda biyar mai karfin megawatts 800.

Kenya ita ce babbar abokiyar cinikayyar Jamus a gabashin Afirka kuma kasa ta farko a nahiyar da ta yi hobbasa a bangaren samar da makamashi mara gurbata yanayi.

Ziyarar Scholz a tashar samar da makamashi a Kenya
Hoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

Shugaban gwamnatin na Jamus da ya kai rangadin tare da rakiyar tawagar yan kasuwar Jamus, ya gana da 'yan kasuwar Kenyan inda sukan tattauna damarmaki na zuba jari tsakanin bangarorin biyu.

Scholz ya ce Akwai kyakkyawan yanayin kasuwanci. Akwai abubuwa da yawa da za a yi amma yana da kyau mu kara zuba jari kai tsaye, kasuwanci da musayar abubuwa. Kuma wannan ba kawai a cikin wadannan fannonin da muke tattaunawa ba, watakila har da samar da makamashi da fitar da abinci da dangoginsa.

A nasa bangaren shugaba Ruto ya shaida wa jagororin sassa daban-daban na kasuwancin cewar, Kenya za ta tabbatar da cewa masu zuba jari sun ci gajiyar kasuwancinsu.

Shugabann Jamus Olaf Scholz a hagu da shugaban Kenya Kenya William Ruto a dama
Hoto: Tony Karumba/AFP

"Za mu yi aiki tare da masana'antu don ganin yadda za mu tafiyar da harkokinmu ta yadda za mu bai wa kowane mai saka hannun jari, walau dan kasar Kenya, ko Jamus, da na sauran kasashen waje, da ma na cikin gida, damar samun kwarin gwiwa kan jarin da suka zuba."

Shigar Jamus a ayyukan makamashi mara gurbata yanayi a Kenya musamman a fagen makamashin Geothermal yana da dogon tarihi. fiye da shekaru 20, Jamus ta na zuba jari a irin wadannan ayyuka, daga cikin wasu ayyuka, ta karkashin bankin raya kasa na KfW da kuma kungiyar kawancen raya kasa ta GIZ. Kazalika Jamus ta kuma zuba jarin miliyoyin kudi a cikin ginin cibiyar makamashi ta Olkaria.

Sai dai har yanzu akwai ayar tambaya dangane da ko Jamus za ta iya cin riba daga shigo da makamashin hydrogen daga Kenya. Ga kasar ta Kenya, duk da haka, fasahar makamashin hydrogen mara gurbata yanayi wajen samar da wutar lantarki zai ba da dama mai girma  da za a ci moriyarsa. Wannan ya hada da samar da takin zamani don aikin noma, sai dai har yanzu ana bukatar iskar gas don samar da makamashin na hydrogen.