1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Duniya na juyayin rashin Sarauniya Elizabeth ta II

September 9, 2022

Sarauniyar Ingila Elizabeth ta II ta rasu bayan gajeruwar rashin lafiya. Cikin wata sanarwa da Fadar Buckingham ta fitar, ta ce sarauniyar mai shekaru 96 ta rasu ne a gidanta da ke Scotland.

https://p.dw.com/p/4GbV3
Queen Elizabeth
Hoto: Andy Buchanan/AFP

Tun dai da ranar wannan Alhamis din takwas ga watan Satumba ne, aka bayar da sanarwar cewa likitoci sun garzaya wajenta domin duba lafiyarta. Ana sa ran sabuwar firaministar Birtaniya Lis Truss za ta fitar da sanarwa nan ba da jimawa ba. Yarima Charles wanda zai gaji mahaifiyarsa bayan mutuwarta, na can na shirin yi wa Birtaniya jawabi. Mutuwar Sarauniya Elizabeth ta II na zuwa ne kwana guda, bayan da ta soke wata ganawa da za ta yi kana likitoci suka shawarce ta da ta huta.

A ranar Talata, marigayiyar ta jagoranci bikin mika mulki ga sabuwar firaministar Birtaniya Liz Truss bayan da tsohon firaministan Boris Johnson ya mika takardar murabus dinsa ga sarauniyar.  A cikin shekarar nan dai sarauniyar ta cika shekaru 70 akan karagar sarautar Ingila, kuma a baya-bayan ta rika wakilta danta Yarima Charles a wasu manyan taruka. Ana sa ran za a ware kwanaki 12 domin bai wa 'yan kasar ta Birtaniya damar jimamin abin da ya faru.