1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Somaliya: Mutane sama da 30 sun halaka

Lateefa Mustapha Ja'afar
June 20, 2023

Rahotanni daga Somaliya na nuni da cewa, kimanin mutane 36 ne suka halaka a sassa dabam-dabam na kasar sakamkon rikici da hare-haren bama-bamai.

https://p.dw.com/p/4SrAt
Somaliya | Rikici | Hare-hare
Somaliya ta saba fuskantar hare-haren 'yan ta'adda Hoto: Farah Abdi Warsameh/AP/picture alliance

Daga cikin wadanda suka rasa rayukan nasu dai, har da wadanda wani rikici da ya barke a jihar Puntland mai kwarya-kwaryan 'yanci ya rutsa da su baya ga wadanda hare-haren bama-bamai da ka kai a yankin Shabelle ya shafa. A Puntland din dai kazamin fadan da ya kaure a Garowe babban birnin jihar, na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan majalisar jihar ke tafka muhawara a kan kundin tsarin gudanar da zabe.