1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan ta Kudu: Salva Kiir zai yi tazarce

Mahmud Yaya Azare LMJ
July 7, 2023

Bayan an kwashe watanni ana zaman jira, daga karshe shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir ya bayyana jadawalin zaben shugaban kasa irinsa na farko a kasar tun bayan da ta samu 'yancin kai daga kasar Sudan.

https://p.dw.com/p/4Tb9a
Sudan ta Kudu | Salva Kiir Mayardit | Tazarce
Jam'iyya mai mulki a Sudan ta Kudu, ta bai wa Shugaba Salva Kiir damar yin tazarceHoto: Brian Inganga/AP Photo/picture alliance

Bayan sanar da jadawalin zaben gama garin da za a gudanar da shi a shekarar 2024, zai bai wa jam'iyyun siyasar kasar 28 da ma 'yan takara masu zaman kansu damar tsayawa takarar shugabancin kasa da na yan majalisun dokoki. Shugaba Salva Kiir na Sudan ta Kudu ya aminta da sake tsayar da shi takara da jagororin jam'iyyarsa suka yi da gagarimin rinjaye, kamar yadda ya bayyana a yayin wani gangami da suka yi. Magoya bayan Shugaba Kiir da ke yi masa kirari da gwarzo a lokacin yaki da lokacin zaman lafiya, sun ce tazarcensa zai bayar da damar aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma a kasar a shekara ta 2017. Ana dai sa ran Shugaba Kiir din zai kara da babban abokin hamayyarsa kuma mataimakinsa Riek Machar wanda duk da bai fito ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara ba, ya sha gindaya wasu sharuddan da ya ce sai sun tabbata ne za a iya gudanar da sahihin zabe a kasar da zai iya shiga a fafata da shi.

Sudan ta Kudu | Riek Machar | Jagoran 'Yan Tawaye
Mataimakin shugaban kasar Sudan ta Kudu kana jagoran 'yasn tawaye Riek MacharHoto: Reuters/M. Nureldin

Shi ma dai wakilin Majalisar Dinkin Duniya a kasar Sudan ta Kudu wanda ya yi lale maraba da sanya jadawalin gudanar da zaben, ya yi kashedin cewa Shugaba Kiir da mataimakin nasa na daukar zaben da ke tafe a matsayin ko a mutu ko a yi rai. A cewarsa lamarin na barazana ga yarjejeniyar zaman lafiyar da ke tangal-tangal, wacca aiki da ita ya kare tun shekara ta 2022. Har yanzu dai ana ci gaba da samun 'yan tashe-tashen hankula a kasar da hatta a shekarar bara, sai da aka halaka fiye da mutane 2000 a rikicin da ya danganci kabilanci da kokuwar samun iko da iyakoki. Masharhanta dai na bayyana cewa wajibi ne Majalisar Dinkin Duniya da sauran al'ummomin kasa da kasa su yi tsayiwar daka, domin tabbatar da ganin zaben na Sudan ta Kudu ya gudana cikin lumana. Wannan kuma na zuwa ne adaidai lokacin da dubu-dubatar 'yan gudun hijirar da ke samun mafaka a kasar Sudan, ke sake komawa gida sakamakon rincabewar rikici a Sudan.