1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta a Sudan

Mouhamadou Awal Balarabe
June 9, 2023

Bangarorin da ke gaba da juna a Sudan sun amince da tsagaita wuta na sa'o'i 24 daga ranar Asabar. Amma Amirka da Saudiyya sun nuna ''bacin ransu'' dangane da rashin mutunta yarjejeniyoyin da aka cimma a baya.

https://p.dw.com/p/4SNw7
Kasar Saudiyya ta saba daukar nauyin taron sulhunta rikicin SudanHoto: AFP

Sojoji Sudan da dakarun sa-kai na RSF sun amince da yarjejeniyar tsagaita bude wuta na sa'o'i 24 da masu shiga tsakani na Amirka da Saudiyya suka taimaka aka cimma. Wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Saudiyya ta fitar ta nunar da cewa, yarjejeniyar da aka sanar bayan wasu jerin wadanda ba a mutunta ta ba, za ta fara aiki a daukacin fadin Sudan daga karfe 6 na safiyar ranar Asabar.

Washington da Ryad sun nuna ''bacin ransu'' dangane da rashin mutunta yarjejeniyoyin da aka cimma a baya. Amma wannan sabuwar yarjejeniya ta zo ne kwana guda bayan ziyarar da sakataren harkokin wajen Amirka Antony Blinken ya kai kasar Saudiyya, wanda ya ba da tabbacin cewa Washington da Riyadh na da burin "ci gaba da hada gwiwa domin kawo kashe fadan da ake yi a Sudan".

Rikicin na Sudan ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 1,800 tare da haifar da munanan matsalar jin kai a kasar da ke zama daya daga cikin mafi talauci a duniya.