1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Madatsar ruwa ta datse a Koriya ta Kudu

Abdourahamane Hassane
July 15, 2023

Mutane bakwai ne suka mutu yayin da uku suka bata sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka shatata a Koriya ta Kudu, jami'an gwamnatin sun ce dubunan mutane sun kaurace wa gidajensu saboda ambaliyar ruwa.

https://p.dw.com/p/4TwU1
Südkorea Wetterl Überschwemmungen im Bezirk Goesan
Hoto: Yonhap/picture alliance

A cikin kwanaki ukun da suka gabata ruwan sama ya mamaye lardunan da dama na Koriyan, inda kafafen yada labaran kasar ke cewa adadin wadanda suka mutu na iya karuwa nan gaba. Sama da mazauna yankin Goesan ta tsakiya dubu shida ne aka umurcesu da su kaura daga yanki, yayin da madatsar ruwa ta yanki, ta fara ambaliya daga mamakon ruwan sama tare da mamaye kauyukan da ke kusa.