1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Rayuwar 'yan gudun hijira a Zambiya

Binta Aliyu Zurmi
August 18, 2023

A Zambiya 'yan gudun hijira da 'yan cirani na nuna damuwa da rashin samun shaidar zama 'yan kasa bayan kwashe shekaru da dama da ma auratayya a tsakaninsu.

https://p.dw.com/p/4VLAa
Malawi | Dzaleka Flüchtlingslager
Hoto: Amos Gumullira/AFP/Getty Images

Mafi akasarin mutanen da suka kwashe sama da shekaru 20 a kasar Zambia da damansu kasar Zambia ita ce suka sani a matsayin kasarsu, kuma basu da niyyar koma wa kasashensu na asali kasancewar sun yi aure sun hayayyafa a kasar, kuma a nan suke sana'o'insu wasu ma har sun mallaki gidaje, to sai dai duk kokarin ganin sun sami takardun zama 'yan kasar ya ci tura.

A wani taron manema labarai a Lusaka 'yan gudun hijirar sun mika kokensu ga Shugaba Hakainde Hichilema ya duba bukatarsu.

"Wani dan jarida Enock Ngoma ya ce Jean Mandela wanda dan gudun hijira ne ya kwashe kusan shekaru 20 a Zambia ya auri 'yar Zambia sun hayayyafa, amma har yanzu ba shi da wata shaida da ke nuna ko shi waye a kasar. Muna kira ga gwamnati da ta duba wannan bukata ta kuma taimaka masa da sauran yan gudun hijira"

Kasar ta Zambia dai yanzu haka ta na da 'yan gudun hijira sama da mutum 100,000 da take basu mafaka, mafi akasarinsu sun fito ne daga Jamhuriyar Dimukradiyyar Kwango mai fama da rikici da Burundi da ma kasar Angola a cewar hukumar 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya.

Wasu 'yan kasar ta Zambia na tausayawa halin da Mandela da ire-irensa ke ciki. Maurice Makalu da ke zama babban darakata a kungiyar Civil Liberties na ganin hanyar da dan kasa ke bi ya samu shaidarsa shi ma bako ya kamata ya sameta a haka. Ya kuma kara da cewa:

"Ya ce duk wani da aka haifa a Zambia ya zauna a kasar na tsawon shekaru biyar zuwa 10 har ya kai shekara 18, ya cancanci zama 'dan kasa muna ganin wannan ya kamata a ce su ma 'yan gudun hijira da suka shafe shekaru 20 zuwa 30 suna da wannan damar"

Abin jira a gani shi ne matakin da mahukuntan kasar za su dauka musamman na yi wa dokar da ake gani na bukatar gyaran fuska.