1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIsra'ila

Dakatar da ba da tallafi wa UNRWA zai kara yin illa wa Gaza

Abdourahamane Hassane
January 31, 2024

Dakatar da ba da kudaden tallafi da kasashe da dama suka wa hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da 'yan gudun hijirar Falasdinu,wato UNRWA.

https://p.dw.com/p/4brM5
Hoto: picture alliance/dpa/APA/ZUMA Press Wire

 Shugabannin kungiyoyin Majalisar Dinkin Duniya da dama sun yi gargadi cewar tsinke bayar da tallafin zai kara saka al 'ummar Gaza cikin wahaloli. A halin da ake ciki a yankin na zirin Gaza da Israi'la ta yi kawanya, sojojinta sun yi kaca-kaca da shi sakamakon hare-haren da suke kai wa da bama-bamai. Abin da ya tilasta wa mutane miliyan daya daga cikin miliyan biyu da rabi  tserewa daga gidajensu, a cewar MDD, sannan ta ce  ana cikin wani mawuyacin hali na rashin abinci da magunguna da ruwan sha. Sai dai ta ce abin takaici ayyukan agajin fararen hula na UNRWA na fuskantar barazana tun a karshen makon da ya gabata bayan da Isra'ila ta zargi ma'aikatanta 12 daga cikin dubu 30,000 na yankin, da hannu a harin da kungiyar Hamas ta  ta kai a ranar bakwai ga watan Oktoba.