1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha tana ci gaba da kai hare-hare Ukraine

January 12, 2023

Rundunar sojin kasar Ukraine, ta ce Rasha ta kai hare-haren da dama a yankunan Donetsk da ke gabashin kasar. Wannan dai sanarwa ce da rundunar sojin ta Ukraine ta fitar.

https://p.dw.com/p/4M3lg
Yakin Rasha da Ukraine
Hare-haren Rasha kan UkraineHoto: AP/Libkos

Yayin da yake karin haske dangane da halin da ake ciki a game da hare-haren da Rasha ta kaddamar a wasu sassa na kasar cikin sa'o'i 24 da suka gabata, mai magana da yawun rundunar sojin kasar Ukraine, Oleksandr Shtupun, ya ce Rasha ta kai hare-haren makamai masu linzami akalla hudu da wasu na jiragen sama 23 baya ga na rokoki da ya ba da kiyasin sun kai 69.

Hare-hare daga Rasha, sun shafi yankunan Luhansk da arewa maso gabashin Kharkiv da Sumy da ma kudancin yankin Zaporizhzhia. Wasu wuraren sun hada da Dnipropetrovsk da kuma kudancin lardin Kherson.

Yakin-Ukraine | Hare-hare
Hare-haren Rasha kan UkraineHoto: Libkos/AP/dpa/picture alliance

Sai dai kakakin rundunar sojin na Ukraine, Oleksandr Shtupun ya ce mayakan saman a kasar sun yi nasarar maida martani kan wasu daga cikin hare-haren na Rasha musamman a yankuna.

Daya daga cikin yankunan da ake tayar da hakarkari a kansa dai shi ne birnin Soledar wanda Ukraine ke cewa ana ci gaba da gwabza fada a cikinsa, yayin kuma da sojojin hayar Rasha na kamfanin Wagner ke cewa su ne ke rike da shi.

Wannan dai na zuwa ne yayin da Rasha ta sanar da nadin Janar Valery Gerasimov a matsayin sabon kwamandan rundunonin hadin gwiwa da ke yaki a Ukraine, inda ya maye gurbin Janar Sergey Surovikin wanda aka bai wa mukamin cikin watan Oktoba na shekarar da ta gabata ta 2022.

Kwace yankin na Soledar dai na iya sauya al'amura cikin watanni 11 na yakin da Rasha ta kaddamar a kan Ukraine din, ganin hakan na iya bai wa dakarun gwamnatin Mosko damar kwace wurare da dama da ke a lardin Donetsk da har yanzu ke ci gaba da zama karkashin ikon kasar Ukraine, musamman ma birnin Bakhmut.