1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta yi amfani da makami mai linzami a Ukraine

December 31, 2022

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce kasarsa ba za ta taba yafe wa Rasha ba kan wadannan hare-hare da ta kai a cikin birnin Kiev da kuma yankin Zaporizhzhya da ya kunshi cibiyar nukiliya

https://p.dw.com/p/4LbYx
Hoto: Vladyslav Sodel/REUTERS

Rasha ta kai wasu munanan hare-hare a Ukraine a yayin da ya rage 'yan sa'o'i kalilan a shiga sabuwar shekara ta 2023. Shugaban Ukraine ya wallafa haka a shafinsa na sada zumunta, yana mai cewa  bai dace hukumomin Moscow su kai wa Ukraine hari da makamai masu linzami ba a daidai lokacin da jama'a ke tsaka da shirin shiga sabuwar shekara.

Ya ce babu wani mutum a doron kasa da zai iya kawar da kai daga wannan abin da ya kira ''danyen aikin'' da fadar Kremlin ta aikata.