1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Rasha ta bude ofishin jakadancin ta a Burkina Faso

December 29, 2023

Rasha ta sake bude ofishin jakadancin ta a Burkina Faso, bayan rufe ofishin na tsawon shekaru 32 da suka gabata, sakamakon yankewar huldar diflomasiyya da aka samu a wancan lokacin tsakanin kasashen biyu.

https://p.dw.com/p/4agct
Hoto: Vladimir Smirnov/TASS/IMAGO

Rasha ta sake bude ofishin jakadancin ta a Burkina Faso, bayan rufe ofishin na tsawon shekaru 32 da suka gabata, sakamakon  takun saka da aka samu a wancan lokacin tsakanin Moscow da Ouagadougou.

Ma'aikatar harkokin wajen Burkina Faso, ce ta sanar da hakan a wata sanarwa da ta fitar, ta ce Rasha ta bude ofishin ta a birnin Ouagadougou, kuma jakadan Rasha a kasar Ivory Coast, Alexei Saltykov, shi ne zai jagoranci ofishin kafin fadar Kremlin ta turo sabon jakada.

Sanarwar ta kara da cewa, duk da an raba-gari na tsawon shekaru 32, amma kawai huldar cinikayya na tsawon wannan lokacin tsakanin kasashen biyu, kasancewar akwai danganta ka mai karfi tsakanin Rasha da Burkina Faso.