1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta sha alwashin karbe ikon Mariupol

Ramatu Garba Baba
March 15, 2022

Mutum guda ya mutu bayan jerin hare-haren Rasha a wannan Talata a Kyiv babban birnin kasar Ukraine. Rasha ta kuma sha alwashin kwace iko da birnin Mariupol.

https://p.dw.com/p/48U76
Ukraine Kiew | Zerstörtes Wohngebäude nach Beschuss
Hoto: Felipe Dana/AP Photo/picture alliance

Rhotanni na cewa wasu jerin hare-haren Rasha sun haifar da munanan gobara a wasu yankunan da ke Kyiv babban birnin kasar Ukraine. Mutum guda aka tabbatar ya mutu baya ga wasu da dama da su makale a cikin manyan gine-ginen da ke ci da wuta. 

Rasha ta kuma sha alwashin karbe iko da birnin Mariupol mai matukar mahinmanci a yayin da aka shiga mako na uku da soma yakin. Mutum fiye da miliyan biyu ne suka zama 'yan gudun hijira a yayin da Majalisar Dinkin Duniya ke ci gaba da fuskantar tsaiko a kokarinta na isar da agaji ga wadanda fadan ya tagayyara.