1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ko sojojin Wagner sun so juyin mulki a Rasha?

June 24, 2023

Shugaban kamfanin Wagner na sojojin hayar Rasha, Yevgeny Prigozhin da ke yi wa Moscow tawaye ya ce mayakan da yake jagoranta sun kwace iko da shelkwatar tsaro ta sojojin Rasha da ke Rostov.

https://p.dw.com/p/4T19P
Hoto: via REUTERS

Rasha ta shiga cikin wani yanayi na rudani a jiya Asabar tun bayan da dakarun sojin hayar kasar nan na kamfanin Wagner suka fara kwace iko da wasu yankuna na kasar.

Shugaban Rasha Vladimir Putin, ya ce kasar na cikin wani gagarumin yakin kare makomarta, yayin da yake zargin kamfanin sojin hayar na Wagner mai mayaka dubu biyar da yunkurin juyin mulki.

Mr. Putin ya zargi shugaban kamfanin na Wagner Yevgeny Prigozhin da cin amanar kasa da zagon kasa da ma shirin kifar da gwamnatinsa.

Daga nashi bangare, shugaban sojojin na haya Yevgeny Prigozhin ya ce ba su da niyyar juyin mulki, kawai dai gangamin neman adalci ne sojojinsa ke yi.

Russland | Wagner-Söldner in Rostow am Don
Hoto: Alexander Ermochenko/REUTERS

Wannan lamari ne da ke faruwa a daidai lokacin da shugabannin kasashen duniya da suka hada da Amurka da Faransa da Jamus da Saudiyya suka tattauna ta wayar tarho kan halin da ake ciki, inda suka kara jaddada goyon bayansu ga Ukraine.

A baya-bayan nan dai Yevgeny Prigozhin ya dauki lokaci yana musayar yawu da jagororin sojin Rasha da ke jagorantar ya?in, lamarin da a yanzu ake ganin ya koma tamkar tawaye.

Bayanai dai daga Rashar na nuna cewa sojojin na Wagner sun fara janyewa daga yankunan da suka kwace, bayan shiga tsakani da shugaban kasar Belarus Nicholas Lukashenko ya yi.