1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton shekara na UNDP kan Afirka

May 15, 2012

Nahiyar Afirka an nuna cewar ita ce tafi fama da matsalar karancin abinci a duniya

https://p.dw.com/p/14vwe
Hoto: picture-alliance/dpa

Hukumar raya kasashe ta majalisar dinkin duniya, wato UNDP,  ranar Talata  a birnin Nairobi, ta gabatar da  rahoton ta na shekara, a game da ci gaban jama'a a nahiyar Afirka, da kuma dangantakar dake akwai tsakanin  matsayin rayuwa da  kokarin nahiyar  take yi na   tabbatar da isasshen abinci ga dukkanin al'ummar wannan yanki. Hukumar ta UNDP tace nahiyar Afirka ba zata sami nasarar ci gaba da  kiyaye bunkasar tattalin arzikin da   take samu a yanzu ba,  saiidan an kawar da matsalar yunwa dake addabar akalla kashi daya cikin kashi hudu na  mazauna nahiyar.

A rahoton da hukumar ta UNDP ta sanya masa suna kokarin  tabbatar da isasshen abinci a Afirka, ta baiyana bakin cikin ganin cewar bunkasar tattalin arziki da ake samu yanzu  a yanzu,  bai taimaka ga  samun karuwar  abinci tsakanin masu bukata ba. Kakakin  hukumar UNDP,  Helen Clark wadda ita ce ta gabatarda rahoton na shekara a birnin Nairobi,  tace maida hankali kan bbatun noma kadai ba zai  warware matsalar karancin abinci a Afirka ba. Ana bukatar  kyautata matakan jin dadin zaman jama'a a  yankunan karkara da kyautata hynyoyin kiwon lafiya da baiwa  kananan manoma damar mallakar gonaki da   taimakon kansu da kansu.

Hukumar UNDP tace abin bakin ciki ne ganin cewar  ko da shike akwai rarar abinci mai yawa a duniya baki daya, amma  yunwa da rashin  isasshen abinci kai gina jiki har yanzu suna addabar mazauna mnahiyar Afrika, musmaman na  kudu da hamadar Sahara a yankin Sahel. Kazalika, duk da bunkasar tattalin arziki da  nahiyar Afrika take samu, amma hakan bai yi jagora ga kyautata bada ilimi ba ko  kyautata jin dadin zaman jama'a da bunkasa samar da abinci.

Logo UNDP United Nations Development Programme
Hukumar raya kasa ta Majalisar Dinkin DuniyaHoto: APGraphics

Nahiyar Afirka, inji rahoton,  shine yankin da yafi fuskantar matsalar  karancin abinci a duiya baki daya, inda  akalla kashi daya cikin kashi hudu na mazauna yankin  miliyan 856 suke fama da yunwa ko karancin abinci mai amfani a jiki. A yanzu haka,  mutane  fiye da miliyan goma sha biyar ne suke fuskantar yiwuwar rasa rayukan su saboda yunwa a yankin Sahel abin da ya hade kasashen Senegal, Chadi,  da jamhuriyar Niger, har ya zuwa yankin kahon Afirka, kamar  Djibuti da Habasha da Kenya ko Somalia.

Helen Clark,  ta hukumar UNDP, wadda ita ce ta gabatar da rahoton ranar Talata, tace  tabbatar da isasshen abinci, kamar yadda  aka shimfida lokacin taron kolin abinci na duniya a shekarata 1996, yana nufin  ko wane dan Afirka ya kasance da damar  samun isasshen abinci kuma mai gina jiki a duk lokacin da yake da bukata, domin tabbatar da rayuwa da koshin lafiyar sa. Tace  ana iya samun nasarar tabbatar da isasshen abincin ga kowa da kowa a Afirka idan aka kiyaye wasu sharudda da suka hada har da  kara bunkasa noma da kawo karshen   rikon sakainar kashi da ake yiwa noman, tare da goyon bayan  mata manoma, wadanda sune  masu samar da mafi yawan  abincin da ake nomawa a Afirka, sai kuma baiwa kananan yan kasuwa da masu sarrafa kayan amfanin gona kwarin gwiwa.

Afrika Lebensmittel - Preise steigen
Hauhawar farashin kayan abinci a AfirkaHoto: AP

Rahoton ya ambaci  kasashe kamar Ghana da Malawi, wadanda yace  sun sami  ci gaba matuka a kokarin su na  cimma burin  Millenium nan da shekara ta 2015, a fannin samarwa jama'ar su isasshen abinci.

Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita: Zainab Mohammed Abubakar