1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTarayyar Rasha

Putin zai gana da Kim Jong Un na Koriya

September 5, 2023

Gwamnatin Amirka ta yi kira ga Koriya ta Arewa da ta kauce wa sayar da makamai ga Shugaba Putin, tana mai tunasar da hukumomin Pyongyang alkawarin da suka dauka na kauce wa sayar da makami ga Rasha a yakin Ukraine.

https://p.dw.com/p/4VxZM
Hoto: Korean Central News Agency/Korea News Service/AP Photo/picture alliance

Wani jami'in gwamnatin Amirka ya ce ya samu bayanan sirrin da ke nuna cewa shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong Un ya shirya ziyartar kasar Rasha domin ganawa da shugaba Vladimir Putin a daidai lokacin da Rasha ke kokarin cefano makamai masu hatsari daga Koriya ta Arewan don amfani da su a yankin da take yi da Ukraine. Jami'in ya ce akwai yiwuwar shugabannin biyu su yi ganawar a cikin wannan wata da muke ciki.