1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikice-rikice na damun Paparoma

Abdoulaye Mamane Amadou
April 9, 2023

A jawabinsa na bukukuwan Ista (Earster) ga mabiya addinin Kirista, Paparoma Francis, ya soki yadda tashe-tashen hankula ke neman mayar da hannun agogo baya ga kwanciyar hankalin duniya.

https://p.dw.com/p/4Pr2y
Vatikanstaat Papst Franziskus, Generalaudienz
Hoto: Massimo Valicchia/NurPhoto/picture alliance

Jagoran darikar Katolika na duniya Paparoma Francis, ya soki yadda tashe-tashen hankula a Ukraine da Gabas ta Tsakiya da hare-haren ta'addancin duniya a matsayin abinda ke mayar da hannun agogo baya ga zaman lafiyar duniya.

A gaban dandazon mabiya darikar Katolika kimanin dubu 100 a wannan Lahadi, babban limamin mabiya addinin Kiristan ya nuna damuwa kan rikicin da ya kunno kai tsakanin Isra'ila da Falasdinu, lamarin da ya kira mummunar barazana ga kokarin sulhunta rikicin bangarorin biyu.

Kana Paparoma Francis, ya nuna alhini ga wadanda suka rasa danginsu a yankin Ukaraine da ma masu yin hijira, tare da mika kira ga kasashen duniya da su yi mai yiwuwa don tabbatar da dorewar zaman lafiya a doron kasa. Babban limamin na jawbin ne, a albarkacin bukuwan Earster na wannan shekara.