1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kwantar da Fafaroma a asibiti

Binta Aliyu Zurmi
June 7, 2023

Rahotanni daga fadar Vatican na cewar shugaban darikar katolika na duniya Paparoma Francis na fama da rashin lafiya, lamarin da ya kai ga kwantar da shi a asibiti a birnin Roma domin yi masa tiyata.

https://p.dw.com/p/4SJ2a
Papst Franziskus
Hoto: Ettore Ferrari/ANSA/picture alliance

Wannan dai shi ne karo na biyu cikin shekara guda da za a yi wa Paparoma aikin tiyata, baya ga ta matsalar hanji da ya fuskanta a watan Yulin shekarar 2022.

Llikitocin da ke duba lafiyar Pararoma Francis mai shekaru 86 sun yanke shawarar sake yi masa tiyata a ciki bisa tsananin ciwon da yake fama da shi.

Sai dai fadar Paparoman ba ta bayyana ko zai soke tafiye-tafiyen da zai yi nan gaba kamar yadda ya wakana a bara ba.

A baya Paparoma Francis ya bayyana cewar a shekarar 2021 ya taba ganin likitan kwakwalwa a kasarsa ta haihuwa Ajantina a lokacin da yake dan matashi, domin taimaka masa wajen magance matsalar damuwa da ta samo asali daga mulkin kama-karya na soja.