1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin bam ya halaka mutane a Pakistan

Lateefa Mustapha Ja'afar
March 4, 2022

Wani mummunan harin bam da aka kai a wani masallacin Musulmi mabiya mazhabar Shi'a a yankin Arewa maso Yammacin Pakistan, ya halaka mutane da dama.

https://p.dw.com/p/481q7
Pakistan | Harin bam a Masallaci I Peshawar
Harin dai ya halaka mutane da dama tare da jikkata wasu masu yawaHoto: Faridullah Khan/DW

Harin na garin Peshawar da ke yankin Arewa maso Yammacin Pakistan din ya kuma yi sanadiyyar raunata mutane sama 60, kamar yadda kwamishinan 'yan sandan yankin Muhammed Ejaz Khan ya tabbatar ga manema labarai. Ejaz Khan ya ce cikin wadanda suka rasa rayukan nasu, har da jami'in dan sanda guda. Wani jam'in dan sanda a yankin Waheed Khan ya nunar da cewa, bam din ya tashi ne lokacin da mutane ke tsaka da salla.