1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun Pakistan ta daure Imran Khan

August 5, 2023

Duk da cewa tsohon firaministan ya musanta laifukan da aka same sa da aikata, hukuncin na nufin da wuya idan zai iya tsayawa takara a zaben kasar da za a yi a cikin shekarar nan.

https://p.dw.com/p/4UoYa
Tsohon firaministan Pakistan Imran Khan
Tsohon firaministan Pakistan Imran Khan Hoto: K. M. Chaudary/AP Photo/picture alliance

Wata kotu a Pakistan ta samu tsohon firaministan kasar Imran Khan da aikata laifin cin hanci, ta kuma yanke masa hukuncin daurin shekaru uku a gidan kaso. Kotun ta ce tsohon firaministan ya nuna rashin gaskiya a zargin da aka yi masa tun da farko, inda ta ce ta gano yadda a tsakanin shekarun 2018 zuwa 2022 lokacin da Khan yake kan madafun iko, ya wawuri wasu kudade da yawansu ya kai kusan Euro 600,000.

Lauyan tsohon firaministan ya ce a safiyar Asabar din nan, jami'an tsaro sun kama Imran Khan din a gidansa da ke birnin Lahore. Biyo bayan wannan hukunci, Khan din ya fitar da wani faifan bidiyo, inda ya bukaci magoya bayansa su kwantar da hankalinsu.