1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin kunar bakin wake ya hallaka mutane 44 a Pakistan

Abdullahi Tanko Bala
July 30, 2023

A kalla mutane 44 suka rasa rayukansu wasu da dama kuma suka jikkata sakamakon harin kunar bakin wake a wajen wani taron siyasa na wata babbar jam'iyyar Islama a arewa maso yammacin Pakistan.

https://p.dw.com/p/4UZLJ
Hoto: Rescue 1122 Head Quarters/AP/picture alliance

An nufi harin ne kan jam'iyyar Jamiat Ulema al Islami JUI-F party wadda ke cikin kawancen gwamnati karkashin jagorancin wani fitaccen malamin addini.

Ministan lafiya na gundumar Khyber Riaz Anwar ya tabbatar da mutuwar mutane 44 yayin da wasu fiye da 100 suka sami raunuka.

Babu kungiyar da ta dauki alhakin harin kawo yanzu sai dai kungiyar IS ta sha kai hare hare kan Jam'iyyar ta JUI-F a baya bayan nan.