1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ouattara:Matakin yaki da sauyin yanayi

Abdul-raheem Hassan
May 9, 2022

Shugaban kasar Côte d'Ivoire Alassanne Ouattara ya aza harsashin samar da kudi dala biliyan daya da miliyan 500, domin fara wani gagarumin shirin samar da abinci da farfado da gandun daji nan da shekaru biyar masu zuwa.

https://p.dw.com/p/4B3YR
Elfenbeinküste Abijan Präsident Alassane Ouattara
Hoto: Präsidentschaft der Republik Côte d‘Ivoire

Shugaba Alassanne Ouattara na Côte d'Ivoire ya bayyana haka ne yayin bude taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 15 wato Cop 15 kan sauyin yanayi a Abidjan babban birnin kasar, inda ya ce shirin zai yi amfani da fasahohi kamar na jirage marasa matuka wajen shuka bishiyoyi da kuma amfani da iri mai jure fari domin gyara kasa.

Kasar Côte d'Ivoire da ke cikin manyan kasashen masu noman ganyén koko a duniya, ta yi asarar kaso 80 cikin 100 na dazuzzukanta kana tana fuskantar hadarin rasa dazuzzukan nan da 2050 idan ba a dauki mataki ba.

Taron na COP15 zai hada kan shugabannin duniya har tsawon makonni biyu, domin tattauna dabarun magance lalacewar kasa da sare itatuwa da kwararowar hamada da ke haifar da fatara da rikici a duniya wanda ya shafi rayuwar mutane fiye da miliyan uku.