1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus na son a saka AU a kungiyar G20

May 4, 2023

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya jaddada goyon bayansa na shigar tarayyar Afrika AU cikin kawancen kasashe masu karfin tattalin arziki na duniya G20.

https://p.dw.com/p/4QvNY
Hoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz na ci gaba da ziyarar kwanaki uku a wasu kasashen Gabashin Afirka, inda tuni ya isa kasar Habasha a yau Alhamis.

A yayin ya ke jawabi a birnin Adis Ababa Scholz ya jaddada goyon bayansa na ganin cewar kungiyar Tarayyar Afirka AU, ta shiga cikin kawancen kasashe masu karfin tattalin arziki na duniya wato G20 yana mai cewa: '' Muna fatan taimakawa kungiyar Tarayyar Afirka na ta samu gurbi a kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki na G20. Hakan zai ba ta damar a ringa damawa ta ita, kuma sakamakon ganin dacewar hakan shine saboda mutumta wannan nahiya mai yawan kasashe kuma wacce al'ummarta ke bunkasa''.

Da ma dai a can baya shugabannin Amurka da na Faransa sun bayyana irin wannan fata na ganin kungiyar AU ta samu kujera a kungiyar ta G20 da har kawo yanzu kasar Afrika ta Kudu ce kadai mamba a cikinta.

A yayin ziyar dai Scholz zai yada zango a ofishin hukumar Tarayyar Afirka da ke birnin na Adis Ababa, domin jin inda aka kwana game da shiga tsakani a rikicin Sudan. 

Scholz zai karkare ziyarar ne a kasar Kenya, inda zai tattauna batun cinikayyar makamashi da Shugaba Wiliam Ruto a kokarin da Jamus ke yi na kawo karshen dogaro da Rasha a wannan fanni.