1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine: Karin makamai daga Norway

Lateefa Mustapha Ja'afar
February 14, 2023

Ministan tsaron Norway Bjørn Arild Gram ya sanar da cewa, kasarsa za ta aika da tankokin yakin nan kirar Leopard 2 guda takwas ga Ukraine, domin kara taimaka mata a yakin da take da Rasha.

https://p.dw.com/p/4NUAo
Ukraine | Yaki | Rasha | Norway | Leopard 2
Norway ta sha alwashin aika tankokin yaki kirar Leopard 2 ga UkraineHoto: Canada Department of National Defence/via REUTERS

Ministan tsaron na Norway Bjørn Arild Gram ya bayyana hakan ne, yayin taron kasashe kawayen Ukraine da aka gudanar a birnin Brussels fadar gwamnatin kasar Beljiyam. Ya kara da cewa Norway din za kuma ta aike da karin motocin yaki da kuma kudi ga Ukraine din, domin ta sayi karin makaman kare kai a yakin da take ci gaba da gwabzawa da makwabciyarta Rasha. A cewarsa yanayin da ake ciki a Ukraine na kara shiga cikin rudu, kuma Kiyv ta dogara ne kawai ga taimakon gaggawa da za ta samu daga kasashen Yamma. A karshen watan Janairun da ya gabata ne Gram ya bayyana cewa kasarsa za ta taimakawa Ukraine din, koda yake bai bayyana adadi ko yanayin taimakon da za ta bayar din ba.