1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wani ya harbe mutane da kwari da baka

Abdul-raheem Hassan
October 14, 2021

'Yan sandan Kongsberg a yammacin Oslo sun kama mutumin da ya kashe mutane biyar da kibiya, amma an ce ba da jimawa ba za a bayyana ko harin na da nasaba da ta'addanci.

https://p.dw.com/p/41ehD
Norwegen | Angriff mit Pfeil und Bogen in Kongsberg
Hoto: Terje Pedersen/NTB/AP/picture alliance

Mutane da dama sun jikkata a harbin da mutumin ya yi musu da kwari da baka a kusa da wani kantin sayar da kayan miya a garin Kongsberg da ke Kudu maso Gabashin kasar.

Yanzu haka dai sauran mutanen da suka ji rauni na  jinya a wani asibitin da ke kusa da inda lamarin ya faru. Rahotannin 'yan sanda na cewa tuni aka kama maharin, kuma bincike ya nuna shi kadai ya aiwatar da harin ba tare da taimakon wasu ba.

Sai dai hukumomi suka ce ya yi wuri a iya tantance ko harin na da alaka da ta'addanci ko wata manufa ta daban.