1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NNPC zai ja da baya daga mamaye fagen man Najeriya

Binta Aliyu Zurmi
June 1, 2023

Kamfanin man fetur na Najeriya NNPC ya ce nan ba da jimawa ba zai janye daga babakeren da ya yi a kan kayayakin man kasar.

https://p.dw.com/p/4S5Im
Nigeria Tankstelle in Abuja
Hoto: AFOLABI SOTUNDE/REUTERS

Wannan na zuwa ne kwana guda bayan da kamfanin ya rubanya farashin litar man fetur a gidajen mai mallakar kamfanin.

Sai dai a tattaunwarsa da wani gidan talabijin a kasar, shugaba kamfanin Mele Kyari ya ce nan ba da jimawa ba farashin zai sauko idan aka sami wasu kamfanoni da za su shiga a dama da su wajensamar da man.

Wannan dai na zuwa ne bayan shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya sanar, a lokacin rantsar da shi cewa gwamnati ta dakatar da tallafin man fetur.

Wanda tun bayan wannan furuci na sabon shugaban ne aka fara samun dogayen layi a gidajen sayar da mai a daukacin kasar.