1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NNPC: Matatar mai ta Fatakwal za ta koma aiki

March 15, 2024

Bayan share tsawo na lokaci ana gwaji kamfanin man tarrayar Najeriya na NNPC ya ce matata mafi girma ta gwamnatin kasar da ke a Fatakwal za ta koma aiki.

https://p.dw.com/p/4dhmN
Erdöllraffinerie in Nigeria
Hoto: Construction Photography/Photoshot/picture alliance

Matatar da ke Fatakwal na tace gangar mai da ta kai 210,000 kullum, adadi mafi girma a tsakanin matatun gwamnatin da ke kasar. Kuma sabon fata ga Abujar da ta share shekara da shekaru tana sayen tattacen main a waje, kuma ke neman hanyar rage kisan kudade na wajen.

Tun a shekara ta 2021 ne dai Abujar ta kaddamar da gyara ta matatar da ta lashe sama da dalar Amurka Miliyan dubu daya da rabi, gyaran kuma da shugaban kamfanin main kasar NNPC Mele kyari ya ce an kammala shi tare da kai wa da kaddamar da ragowa na gwaji.

Shekaru biyar can baya ne dai kamfanin ya rufe matatar da ke zaman daya a cikin guda hudu na mallakin kasar.

Kamfanin matatar mai a Najeriya
Hoto: Construction Photography/Photoshot/picture alliance

Ana saran fara tace ganga 60,000 a kusan kullum kafin daga baya a daga adadin zuwa 210 can cikin tsakiya ta shekarar bana.

Engineer Mohammed lawal tsohon darakta a kamfanin NNPC yace fara aikin matatar na iya sauya da dama cikin masana'antar man kasar mai tasiri.

Tarayyar Najeriyar dai na kashe dalar Amurka tsakanin miliyan dubu 25 zuwa dubu 30 a shekara wajen shigo da tattaccen man fetur. Adadin kuma da ke da tasirin gaske wajen hauhawar farashin dala a cikin kasar.

Matatar mai ta Najeriya
Hoto: Construction Photography/Photoshot/picture alliance

Ana dai kallon fara aikin matatar ta Fatakwal da yar uwarta ta Dangote da ke birnin Legas dai na iya kai wa ya zuwa kai karshen shigar da mai da kila ma sauya farashin dala.

Kokarin sake tashin matatar dai na zaman zakaran gwajin dafi ga tarrayar Najeriyar da ke tsakanin cefanar da tsohon kaya da kuma mai da tsohuwa yarinya. Kuma tuni Kamfanin NNPC ya tsara mika harkokin tafiyarwa ta matatar, zuwa ga kamfanin da ke zaman kansa a tarayyar Najeriyar da nufin kauce wa hancin da yai nasarar durkushe daukacin matatun guda hudu.

Nasarar tafi da fatakwal din na iya kai wa ya zuwa mai da hankali ga ragowar guda Ukun da ke Warri da birnin Kaduna a sashen arewacin kasar.