1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar za ta rungumi wata fasahar samun makamashi

Gazali Abdou Tasawa M. Ahiwa
December 23, 2022

Nijar ta kaddamar da shirin fara amfani da fasahar sarrafa takin gargajiya domin samar da makamashi. Shirin da kasar Holland ta dauki nauyi na son samar da makamashi a karkara.

https://p.dw.com/p/4LNer
Hoto: DW

Shirin wanda aka fi sani da African Biodigesta Component, ko Composante Africaine pour le Biodigesteur a Faransance, na da burin taimakawa ga samar da tsaftataccen makamashi musamman a yankunan karkara na kasashen Afirka a farashin ragon malam, da yaki da sauyin yanayi da kuma gurbatar muhalli kamar dai yadda malam Ibrahim Yakouba ministan makamashi na kasar Nijar ya yi karin bayani a jawabinsa na kaddamar da shirin.

Taron kaddamar da shirin samar da makamashin ta hanyar sarrafa takin kagilo da ba haya, ya samu halartar kungiyoyin farar hula da ke fafutikar samar da makamashi a kasar ta Nijar. Kuma Malam Issa Rabiou na Kungiyar CODDAE ya yi mana karin bayani kan wannan fasahar samar da makamashi da kuma takin zamani.

Tun dai ma kafin kaddamar da wannan shiri a hakumance wasu ‘yan kasar ta Nijar suka fara gwajin wannan fasaha. Madame Boureima Maimouna, daraktar babbar rigar Azagou a Nijar ta bayyana fa’idar da ta samu ta hanyar amfani da wannan fasaha.

‘‘Da murahunana guda uku na sarrafa kanjilon, nakan samar da gaz da yawan sa ya kai kubik mita 19 a kowane yini. Kuma makamashin da gaz din ke samarwa tsaftatacce ne. Muna amfani da shi wajen yin girkin abinci da wasu ayyuka kamar na yin walda a cikin rugar tamu. A yanzu a rugata muna samun kangilo daga shanu kimanin 300. Dan haka nake da wani shiri wanda nake son kaddamarwa tare da taimakon masu hannu da shuni ta yadda zan dunga samar da akalla ton dubu na takin zamani ta hanyar fasahar ta biodigester da kuma yadda zan iya kai ga soma sayar makamashin da nake sarrafawa ga gwamnati

Wannan shiri na sarrafa taki domin samar da makamashi  wanda kasar Hollande ke daukar nauyi, na da burin wadatara da akalla mutun dubu 110 da makamashi a kasashen Burkina Faso Mali da Nijar, nan zuwa shekara ta 2025. Wannan shiri na sarrafa taki domin samar da makamashi wanda kasar Hollande ke daukar nauyi, na da burin wadatara da akalla mutun dubu 110 da makamashi a kasashen Burkina Faso Mali da Nijar, nan zuwa shekara ta 2025.