1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

OCHA: Dawo da kai kayan agaji a Nijar

Lateefa Mustapha Ja'afar
November 15, 2023

Majalaisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa jiragen kai kayan agajin jin-kanta zuwa Jamhuriyar Nijar sun koma bakin aiki, bayan dakatar da aikin da suka yi a watan Yuli akamakon juyin mulkin da sojoji suka yi.

https://p.dw.com/p/4Yqlf
Nijar | Agajin Jin-Kai | Majalisar Dikin Duniya | Louise Aubin
Shugabar OCHA ta yankin yammacin Afirka, Louise AubinHoto: DW

Hukumar Kula da Agajin Jin-Kai ta Majalisar Dinkin Duniyar OCHA ce ta sanar da hakan ga kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP a Yamai fadar gwamnatin Jamhuriyar ta Nijar, inda ta ce takwararta mai kula da jiragen saman da ke kai kayan agajin jin-kan UNHAS ta koma aiki a kasar da al'ummarta kimanin miliyan hudu ke matukar bukatar tallafi.