1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Yan farar hula sun yin kiran adalci

April 8, 2021

'Yan kungiyoyin farar hula a Jamhuriyar Nijar sun nuna damuwa kan abinda suka kira rashin mutunta mata wajen kason mukamai a majalisar ministoci.

https://p.dw.com/p/3rkS9
Nigeria I Präsidenten Mohamed Bazoum
Hoto: Facebook/Präsidentschaft der Republik Niger

Sabanin tsohon shugaban kasa Muhammadu Issoufou da ya gama wa'adin mulkinsa na shekaru 10 dukkanin gwamnatocinsa da ya nada majalisar ministocin basa kasa mutum 40 Malam Musa Changari daya daga cikin shugabannin kungiyoyin farar hula ya yi tsokaci.

"Mu burin mu shi ne mutanen da aka zama su zam mutane ne wadanda za su tsaya su yi wa kasa aiki su yiwa talakawa aiki kuma su bi ka'idojin aikin da aka sa su".

Batun cin hanci da kare masu laifuka a wajen doka abu ne da shugabannin kungiyoyin farar hula suka yi Allah wadai da shi. Nasiru Saidu shugaban daya daga cikin kungiyoyin farar hula Muryar talaka ya yi bayani.

"A hukunce shugaban kasa ya fada cewa zai fuskanci yaki da cin hanci a saboda hka ya kamata ya nuna ba sani ba sabo idan aka sami wani ya ci dukiyar kasa. A saboda haka za mu sa ido mu ga irin matakin da zai dauka da kuma hukumar da zai kafa ta yaki da cin hanci da rashawa da kuma irin goyon bayan da zai bata domin ta gudanar da aikinta."

Baya ga rage yawan mambobin majalisar ministoci shugabannin kungiyoyin farar hular sun shawarci shugaban kasa ya duba yiwuwar rage yawan masu bada shawara a fadar shugaban kasa. Sun baiyana fatan gwamnatin za ta aiki bil hakki da gaskiya.

Sai dai kuma kungiyoyin farar hular sun nuna damuwa kan rashin mutunta kason da aka kebewa mata na kashi 30 cikin dari a majalisar ministoci.