1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Nijar ta umarci yan sanda su fitar da Jakadan Faransa

Gazali Abdou Tasawa
August 31, 2023

Ma'aikatar harkokin wajen Nijar ta bai wa hukumar 'yan sanda umurnin fitar da jakadan Faransa Sylvain Itte daga kasar ta hanyar tasa keyarsa

https://p.dw.com/p/4VorV
Nijar | 'Yan sanda sun ja da-ga
Nijar | 'Yan sanda sun ja da-gaHoto: Balima Boureima/picture alliance/AA

Kasar Nijar din dai ta sanar da soke takardar visa da kuma sauran takardun diflomasiyya na jakadan kasar ta Faransa da iyalansa. Wannan mataki na zuwa ne kwanaki hudu bayan da wa'adin kwanaki biyu da hukumomin Nijar suka bai wa jakadan na ya fice daga kasar ya cika.

Jama'a sun yi dafifi a kofar ofishin Jakadancin Faransa a Yamai
Jama'a sun yi dafifi a kofar ofishin Jakadancin Faransa a YamaiHoto: AFP

A wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen ta aika wa Faransa ta sanar da ita wannan mataki na bai wa hukumar 'yan sandan Nijar umurnin fitar da jakadan na Faransar a Nijar Sylvain Itte daga kasar ta hanyar tasa keyarsa. Matakin ya kuma tanadi cire masa rigar kariyar diflomasiyya da soke takardar Visa da duk takardun diflomasiyya na jakadan kasar ta Faransa da ma iyalansa. Da yake tsokaci kan wannan mataki, Malam Bana Ibrahim dan kungiyar fararar hula da ke goyon bayan juyin mulkin a Nijar, ya ce matakin ya yi daidai da bukatunsu na neman raba gari da Faransa.

Nijar | Janar Abdourahmane Tiani
Nijar | Janar Abdourahmane TianiHoto: Balima Boureima/Reuters

Da take mayar da martani ma'aikatar harkokin wajen Faransar ta ce jakadan na ta ba zai yi biyayya ba ga umurnin hukumomin mulkin sojan ba domin a cewarta haramtacciyar gwamnati ce da ba ta da hurumin daukar wannan mataki. To ko wace fassara za a iya yi wa wannan takun saka tsakanin Nijar da Faransa kan batun jakadan.

Karin Bayani: ECOWAS: Sojojin Nijar su mika mulki cikin wata tara

Sai dai Malam Souleimane Brah na babban dakin shawara na ‘yan jaridar Nijar na Maison De la Presse, cewa ya yi akwai bukatar hukumomi da sauran 'yan kasa su yi taka tsan-tsan kan wannan batu domin kauce wa bai wa Faransa damar kaddamar da yaki a kasar.

Yanzu haka dai hukumomin mulkin sojan kasar ta Nijar sun karfafa matakan tsaro a bakin ofishin jakadancin kasar ta Faransa a birnin Yamai inda aka girke a kalla motoci 10 shake da jami'an tsaro a cikin damara.