1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar ta bukaci tawagar EUCAP ficewa daga kasar

Binta Aliyu Zurmi
March 1, 2024

Sojojin wanzar da zaman lafiya na kungiyar Tarayyar Turai a kasashen Sahel EUCAP na shirin kwashe inasu-inasu don ficewa daga jamhuriyar Nijar cikin gaggawa, biyo bayan rashin jituwa tsakaninsu da gwamnatin sojin kasar.

https://p.dw.com/p/4d3S2
Niger | Antje Pittelkau | Polizistin | EUCAP
Hoto: Marou Madougou Issa/DW

A cewar sanarwar da mai magana da yawun kungiyar EU ta fidda, ta ce mahukuntan kasar sun bukaci tawagar ta EUCAP da ta hanzarta ficewa daga kasar, kazalika ta kara da cewar bisa wannan dalilin dakarun za su koma gida nan ba da jimawa ba. 

A watan Disambar bara ne sojoin da ke rike da madafun iko a Nijar suka soke alaka da wannan runduna da ma 'yar uuwarta ta EUMPM, wanda a baya ya kamata a kammala ficewarsu a watan Mayun da ke tafe.

Ko a makon da ya gabata, kungiyar Tarayyar Turai ta nuna rashin jin dadinta biyo bayan wani sumame da aka kai a shalkwatar EUCAP da ke Yamai inda ta ce an kwashe wasu muhimman kayayyakin aikin dakarun.

Kungiyar EUCAP Sahel wacce aka samar da nufin taimaka wa kasashen yankin Sahel yaki da ta'addanci a jamhuriyar Nijar ta na da jami'ai kusan 130.