1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Sulhu tsakanin manoma da makiyaya

November 9, 2023

Kwararrun masana kan harkar noma da kiwo tare da wakilan kungiyoyin manoma da makiyaya a birnin Maradi na Jamhuriyar Nijar sun bayar da shawarwarin kare aukuwar rikicin manoma da makiyaya.

https://p.dw.com/p/4YdcE
Taron sulhu tsakanin manoma da makiyaya
Taron sulhu tsakanin manoma da makiyayaHoto: DW/L. Mallam Hami

A wani mataki na riga kafin aukuwar rikici tsakanin manoma da makyaya da ke haddasa hasarar rayuka, masu ruwa da tsaki kan noma sun bayar da shawarar tsayar da wa'adin sakin gonaki yadda manoma za su kamalla girbin amfanin gonarsu kafin makiyaya su shiga  don kare aukuwar rigima.

shirya wanan taro na mahawara domin tsayar da wa'adin sakin gonaki na 2023 kamar yadda aka saba kowace shekara. 

An dai tafka mahawara kuma an gaya ma juna gaskiya kowa ya bada tasa shawarar kuma a karshe an samu masalaha manoma, da makyayan kowa ya amince da wadanan ranaiku na 3O ga watan Nuwamba yankin Bermo da kuma 20 ga watan December sauran yankunan jaha. Hardo Lalwi Pigyade wakilin makiyayan gundumar Tasawa yace sun ji dadin tsayar da wadannan ranaiku.

Suma daga nasu bangare manoma sun bayana gamsuwarsu.

Hukumomi sun yi gargadi ga duk wanda aka ya taka wannan doka. Sai dain abin jira a gani shi ne tasirin da matakin zai yi wurin hana sake aukuwar rikici tsakanin manoman da makiyaya.