1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yadda ‘yan Nijar ke kallon nadin sabon firaministan kasar

Gazali Abdou Tasawa MNA
April 6, 2021

A Nijar 'yan kasar ne suka soma tofa albarkacin bakinsu a game da sabon Firamnista Ouhoumoudou Mahamadou wanda shugaban kasa Mohamed Bazoum ya nada a karshen mako domin jagorantar gwamnatinsa.

https://p.dw.com/p/3rdUd
Niger | Ouhoumoudou Mahamadou
Hoto: PNDS Tarayya Partei

An haifi Mahamadou Ouhoumoudou sabon firaministan kasar Nijar a shekara ta 1954 a Amaloul ta karamar hukumar Afalla ta cikin Jihar Tahoua. Bayan kammala firamare da sakandare a Nijar, neman ilimi  mai zurfi ya kai shi a kasashen Togo da Faransa da Amirka, inda ya samu takardun diploma da shaifdar ilimi a fannoni dabam-dabam da suka hada da na tattalin arziki da gudanar da kudade, nazarin harkokin siyasa da kuma na jagorancin ma'aikatu na gwamnati da kamfanoni.

Karin bayani: Bazoum zai yi aiki da kasashe makwabta

Bayan kammala karatu ya riki mukamai dabam-dabam a ofishin ministan kudi da babban darakta a kamfanin hakar kwal ko gawayi na kasa na SONICHAR, babban darakta a kamfanin rumbin tsimin cimaka na kasa wato OPVN, babban darakta a bankin kasa da kasa na Afirka wato BIA. Ya zamo ministan ma'adanai da raya kamfanoni da kuma babban daraktan fadar shugaban kasa. A waje ya riki mukamin mataimakin sakataren gudanarwa na ECOWAS da kuma kula da harkokin kudi na kungiyar da dai sauran mukamai na kasa da kasa.

Ra'ayin 'yan Nijar ya bambanta kan nadin sabon Firaminista Ouhoumoudou Mahamadou
Ra'ayin 'yan Nijar ya bambanta kan nadin sabon Firaminista Ouhoumoudou MahamadouHoto: PNDS Tarayya Partei

Sai dai kuma tuni nadin sabon firamnistan ya soma haddasa mahawara a tsakanin 'yan kasa kan dacewa ko rashin dacewar sabon firamnistan. Malam Nasiru shugaban kungiyar muryar talaka na ganin kasancewa sabon firamanistan na da balshe a baya ya sa suke da shakku kan nadin nasa amma tare da fatan zai sauya hali.

Karin bayani: Nijar: Bazoum ya sha rantsuwar kama aiki

To sai dai da take tsokaci kan kan nadin Firamnista Mahamadou Ouhoumoudou jam'iyyar PNDS Tarayya mai mulki ta bakin sakataren kula da harkokin sadarwarta Malam Iro Sani, bayyana dacewarsa ya yi.

Su ma dai wasu mazauna birnin Yamai sun bayyana ra‘ayinsu kann nadin sabon firamnistan da kuma abin da suke jira daga gareshi.

A nan gaba ne dai sabon firamnista Mahamadou Ouhoumoudou da ke zama Firamnista na 19 tun bayan da Nijar ta zamo jamhuriya a shekara ta 1958, zai bayyana a gaban majalisar dokoki inda zai sha rantsuwa kama aiki kafin daga karshe ya kafa gwamnatinsa.