1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hama Amadou na gidan kaso

Gazali Abdou Tasawa
March 2, 2021

Hukumomin na zargin Hama Amadou da aikata laifuka kimanin 10 da suka hada da yunkurin kifar da zababbiyar gwamnati.

https://p.dw.com/p/3q6aP
Hama Amadou
Hoto: picture-alliance/dpa/K. Gabbert

A Jamhuriyar Nijar, madugun adawa Hama Amadou tsohon firaminista kana tsohon shugaban majalisar dokoki ya kwashe kwanansa na farko a gidan kaso a garin Filingue inda hukumomin shari'a na kasar suka kartami shi bayan sun saurare shi a yammacın jiya.