1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Gwamnati za ta binciki kwangilolin ma'adanai

Salissou Boukari
January 23, 2024

MInistan ma'adanai na Nijar ya bayar da umarnin dakatar da kulla sabbin yarjeniyoyi kan ma'adanai tare da umarnin gudanar da bincike kan kwangilolin ma'adanai da aka bayar a baya.

https://p.dw.com/p/4baaL
Hoto: Maurice Ascani/Areva/AP Photo/picture alliance

Umarnin dakatar da bayar da sabbin kwagilolin hakar ma‘adinai da yin nazarin dukannin wadanda aka bayar a baya domin sanin inda dosa a cikin sabuwar tafiya da kasar ta sa a gaba domin yan kasa su sami haske a kan wannan fanni. Magatakardar ofishin ministan kula da hakar ma'adinan karkashin kasa ta ce wannan ba abu ne da zai daga hankali ba.

Karin Bayanai: Inganta hakar ma'adanai a Jamhuriyar Nijar

Tun shekaru da dama dai kungiyar farar hula ta ROTAB da ke sa ido kan arzikin kasa ta ke yin hannunka mai sanda ga gwamnati ta yadda arzikin zai amfani yan kasa. Aissami Tchiroma na kungiyar ta ROTAB ya yaba wa wannan mataki da ya ce yana cikin manyan bukatun yan kasa:

Karin Bayani: Kalubalen aikin hakar uranium a Nijar

Su ma kungiyoyi da ke fafutikar nuna kishin Afirka irin su AJPR sun ce abu ne da ya kamata yan kasa sun san abubuwan da ke wakana a fannin arzikin da ake hakowa na karkashin kasa kamar yadda shugaban kungiyar Mourtala Abdou Aziz Nafiou ya nunar.

Tuni dai ofishin ministan da ke kula da hakar ma'adinai ya ce zai danka wa kwararru a fannin hakar ma'adinai yin nazarin halin da ake ciki domin al'ummar Nijar ta rinka samun cikakken bayanai a kan yawan ma'adinain karkashin kasa da ake fitarwa kamar zinariya da kuma ribar da kasar ke samu.