1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Faransa ba su iya shiga Nijar sai da izini

Gazali Abdou Tasawa AH
April 2, 2024

A Jamhuriyar Nijar hukumomin mulkin sojan kasar sun dauki wani sabon mataki wanda ya tanadi tilasta wa Faransawan da ke aiki ko yin balaguro a cikin kasar, mallakar takardar izinin yawo a cikin kasar.

https://p.dw.com/p/4eLqQ
Hoto: Sam Mednick/AP Photo/picture alliance

Tun dai bayan raba gari da   Nijarta yi da Faransa biyo bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yulin 2023 da kuma zaman doya da man jan da ya biyo baya , hukumomin mulkin sojan kasar ke ta daukar matakai daya bayan daya na abin da suka kira rigakafin kare kasar daga duk wani yunkuri na zagon kasa da Faransar ta sha alwashin yi wa mulkin sojan kasar.

Nijar na da shaku a game da shigar Faransawa a kasar

Niger I Fluggäste vor dem internationalen Flughafen Diori Hamani in Niamey
Hoto: AFP

Bayan kama wasu tarin makami a wani gidan da sojojin Faransa membobin rundunar tsaro ta Turai a Sahel wato   EUCAP Sahel suka yi zama a birnin Yamai kafin ficewa daga kasar mahukuntan kasar suka karfafa matakai sa ido ga Faransawa da ke shigi da fici a kasar. Yanzu haka dai baya ga takardar izinin shiga kasar ta biza da kuma takardar talaguro ta fasfo, hukumomin mulkin sojan kasar sun tilasta wa Faransawa masu shigowa kasar da sunan aiki ko kuma ziyara ko yawon buda ido izinin mallakar takardar izinin yawo cikin gari ko   cikin kasa 

Tsananin bincike a filayen jiragen sama domin tantance masu shiga Nijar

Niger Evakuierung der ausländischen Staatsbürger/Niamey Flughafen
Hoto: Stanislas Poyet/AFP

Bayanai dai sun tabbatar da cewa mahukunta sun tsaurara binciken  Faransawa a filayen jiragen sama na kasar inda a wasu lokuta aka tilasta wa wasu faransawan koma daga inda suka fito matsawar ba su mallaki wannan takarda ba ta izini. Sai dai Malam Amadou Roufa’i Lawel Sallaou wani dan fafutika a Nijar na ganin akwai bukatar yin Sassauci ga Faransawan da ke shigo wa kasar da suna  aikin agaji inda yanzu haka kungiyoyin agaji sama da 30 na Faransa ke ci gaba da aiki a kasar.