1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gano gawawaki a hatsarin jirgin sama

Binta Aliyu Zurmi
May 31, 2022

Mahukunta a Nepal sun tabbatar da samun dukkanin gawawakin mutanen da suka mutu a hatsarin jirgin saman da ya auku a karshen makon da ya gabata.

https://p.dw.com/p/4C4Zh
Nepal | Flugzeug Tara Airline | Absturzstelle
Hoto: Fishtail Air Pvt Ltd/REUTERS

Da safiyar wannan rana ta Talata ce mahukunta a kasar ta Nepal suka tabbatar da samun gawawakin mutane 22 da suka mutu a wani hatsarin jirgin sama a da ya auku a kasar.

Sanarwar ta kara da cewar tuni aka fara bincike don tantance gawawakin domin mikasu ga iyalansu. 

A ranar Lahadin da ta gabata ce wani karamin jirgin daukar masu yawon bude ido ya fadi jim kadan bayan tashinsa zuwa yankin nan na Jomsom da 'yan yawon bude idanu kan ziyarta.