1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar ta yi ikirarin nasara

Mahaman Kanta
May 13, 2022

Ministan cikin gidan Nijar Hama Souley Adamou ya baiyana samun nasarori a yakar ayyukan ta'addanci da ake yi a wasu yankunan Diffa da Tillaberi.

https://p.dw.com/p/4BHGo
Symbolild Niger Islamistischer Terrorismus
Hoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

A yayin da yake wa majalisar dokoki bitar sakamakon matakan da gwamnati ta dauka, ministan ya ce akwai nasara amma a nasu waje shugabannin kungiyoyin farar hula sun ci gaba da adawar kasancewar dakarun ketare a Nijar.

Jihar Tilleberi na Nijar din dai, nan ne rashin tsaro ya fi kamari, inda mayaka ke ci gaba da kai hari kan hanyoyin sadarwa na tafi da gidanka da hukumomin samar da makamashi inda ta nan ne ake kaiwa jama'a wutar lantarki zuwa gidajensu, daura da dashe dahen boma bomai da kwanton bauna ga matafiya.

Mahukuntan Nijar din a ta bakin ministan kula da harkokin cikin gida dai, ya ce lamura sun fara kyau duk da cewar a kwai wasu yankuna da ke kan iyakar Nijar da Burkina Faso da ake fuskantar tashe tashen hanku.