1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta yi watsi da rahoton EU kan babban zabe

Ubale Musa Abdoulaye
July 3, 2023

A daidai lokacin da kotuna a Najeriya ke ci gaba da zama sauraron korafe-korafen zabukan kasar, wani rahoton da masu kallon zabe daga kungiyar tarayyar Turai suka fitar na tada kura

https://p.dw.com/p/4TMv9
Najeriya | Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Najeriya | Shugaba Bola Ahmed Tinubu Hoto: Sunday Aghaeze/Nigeria State House via AP/picture alliance

Masu sa ido a zaben Najeriya da kungiyar tarayyar Turai ta aike don sa ido kan yadda zaben ke tafiya sun shafe tsawon kwanaki suna yin nazari kan zaben gabanin fitar da rahoton da ya haifar da kace-nace a fagen siyasar Najeriya yanzu haka.

 Kungiyar EU ta ce zaben na cike da kura-kurai da son zuciya, ko bayan kokarin murde wuya dama fadin ko namu ko kafar katako, a yayin da ita kuma gwamnatin Najeriya ke fadin rahoton na zaman kokarin kitso da kwarkwata ga tarrayar Najeriya da ke samun gaggarumin ci-gaba cikin demokaradiyya.

Wata sanarwar fadar gwamnatin kasar ta ce ba inganci a rahoton, a cewar Abdulazeez Abdulazeez daya daga cikin kakakin gwamnatin Najeriya "Rahoton na kokarin yi wa gwamnatin kasar manakisa ne."

Kokarin kutse a cikin kallon zabe ko kuma tona asirin magudi a siyasa, irin wannna sakamakon rahoton ne ya kai ga tsohuwar gwamnatin Umaru Yar’Adua kafa kwamitin mai shari'a Lawal Uwais da nufin nazarin tsarin zaben, sakamakon rahotannin da ke tabbatar da ha'inci kan nasarar PDP a zabe na shugaban kasar na shekara ta 2007.

Mahukuntan Najeriyar sun dauki lokaci suna kallon turawan yammacin duniya da idanun zargi da kila ma kokari na dakile duk wani ci-gaban da kasar ke fatan samu walau a tattali na arziki koko siyasa.