1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Shell zai biya diyyar malalar mai

Abdullahi Tanko Bala
December 23, 2022

Kamfanin mai na Shell zai biya diyyar euro miliyan 15 ga wasu al'umomi a yankin Niger Delta na Najeriya da ya gurbata musu muhalli a sakamakon fashewar bututu da ya haifar da tsiyayar mai.

https://p.dw.com/p/4LNK2
Ölquelle in Nigeria Flash-Galerie
Hoto: picture alliance/dpa

Bayanan biyan diyyar na kunshe ne a wata sanarwar hadin gwiwa tsakanin kamfanin man na Shell da kungiyar kare muhalli ta Friends of the Earth.

Biyan diyyar dai ta biyo bayan wata kara ce da kungiyar masu rajin kare muhalli ta Friends of the Earth ta shigar a gaban wata Kotu ta kasar Netherlands da ke kalubalantar kamfanin na Shell na Nigeria da alhakin tsiyayar man a 2022 inda kuma kotu ta bukaci kamfanin ya biya diyya ga manoman da aka lalata wa gonakinsu.

Kudin zai amfani al'umomin Oruma da Goi da Ikot Ada Udo a Najeriya wadanda tsiyayar mai daban daban har sau hudu ta yi wa mummunar illa a tsakanin shekaru 2004 da kuma 2007