1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya za ta karkata kan arzikin ma'adinai

September 4, 2023

Bayan tsawon shekaru na dogaro kan man fetur, gwamnatin taraiyar Najeriya ta kama hanyar komawa zuwa ma'adinai na karkashin kasa cikin neman tsira.

https://p.dw.com/p/4Vx1R
Hakar ma'adinai a BauchiHoto: DW/Aliyu Muhammed Waziri

Kama daga Zinariya zuwa ga Azurfa ko bayan Karfe da ma fararkasa, ma'adinai sama da 40 ne dai tarrayar Najeriyar take tunkaho kai.

Kuma bayan daukar tsawo na lokaci tana ta karkata bisa man fetur, sabbabin 'yan mulki na kasar sun ce hankalinsu zai koma ya zuwa ma'adinan da kasar ke fatan na iya dora ta a kan hanyar tsira. Kusan rabi na arzikin taraiyar Najeriyar ne dai, Abujar ke fatan samu daga arzikin ma'adinan da ke warwatse a ko'ina cikin kasar a halin yanzu.

Kuma tuni kasar ta ce za ta kafa wani babban kamfani da ke da shigen NNPC da ke kula da harkar man fetur da nufin yin ciniki da goga kafada a fadar Dele Alake da ke zaman ministan harkokin ma'adinan kasar:

Agadez Nigeria Flüchtlingslager
Jami'an tsaro a inda ake da ma'adinaiHoto: Getty Images/AFP

"Dole ne ma'aikatar ma'adinai ta yi hobbasa in har tana da bukatar cin moriyar arzikin ma'adinan na triliyan na dalar Amurka da ke a karkashi na kasarta. Dole ne a samu sauyin tsari da dabaru, ta sake fasalin  ma'aikatar ma'adinan domin kaiwa zuwa ga bukata ta kasa. Daga cikin dabarun kaiwa zuwa ga bukatar na zaman samun jari na kasa da kasa daga ingattatu na bayanai da kowa ke iya samu. A ko'ina a duniya , hakar ma'adinai babbar harka ce ta kasuwa. A saboda haka taraiyar Najeriya dole za ta jaddada matsayi kan wannan tare da kafa babban kamfanin da zai yi kasuwa cikin harkar ma'adinan shigen abun da ya faru cikin masana'antar man fetur ta kasar mu. A saboda haka, ma'aikatar mu tana shirin kafa babban kamfani da zai taka rawa a cikin wannan harka.

Wannan kamfani zai yi kasuwa cikin tanaje tanaje guda Bakwai dake bukatar saiti a cikin gaggawa."

Karkata zuwa ma'adinan dai na kara fitowa fili da irin girman kalubalen da ke gaban mahukuntan taraiyar Najeiryar da daga dukkan alamu ke shirin dawowa daga rakiyar danyen mai. Man da ya dauki kasar na shekara da shekaru dai, tuni ya fara nuna alamun gaza daukar  bukatun cikin kasar da ke ta karuwa a halin yanzu.

Babu dai damar rance a yayin kuma talaucin cikin kasar ke neman mai dda haraji kurar baya cikin tunanin yan mulkin. To sai dai kuma a fadar Dr Isa Abdullahi da ke zaman kwararre bisa batu na tattali na arzikin sabuwar dabarar 'yan mulkin na iya kai wa ya zuwa sauya da dama cikin kasar a nan gaba.

Nigeria Bauchi Bergbau
Masu hakar ma'adinai a BauchiHoto: DW/Aliyu Muhammed Waziri

Kokari na arzikin dare daya ko kuma kara nisa a cikin rudun rashin kudi, kama daga sashen Arewa maso Yammacin kasar ya zuwa tsakiyarta dai, kusan mafi yawa na wuraren ma'adinan na zaman tungar rashin tsaro a halin yanzu. Rashin tsaron kuma d aya kalli kisan kudi ba adadi a lokaci mai nisa ba tare da kaiwa zuwa ga bukata ta masu mulki na kasar ba.

Ana ma dai kallon ma'adinan na dada rura wutar rikici a cikin taraiyar Najeriyar in da masu aikin hakar ma'adinan ko dai ke cikin rikicin rashin tsaron , ko kuma sun kafa nasu jami'an tsaron kafin nasarar aikin. Abun kuma da ya sa da kamar wuya iya dauka ta hankali na kamfanoni na waje da ke kwadayin zuba jari cikin kasar amma kuma ke tsoron rashin tsaron a halin yanzu.

Dr Yahuza Getso dai na sharhi cikin batun rashin tsaron, kuma ya ce bukata ta kudi a banagren 'yan mulkin na iya sauya halin rashin tsaro na yankunan hakar ma'adinan a nan gaba. Ya zuwa yanzun dai batun hakar ma'adinan na zaman daya tilo cikin kasar da ke da bukata ta kudi amma kuma ke kallon karuwa ta toshewa ta kafofin kudin kasar a halin yanzu.