1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: NNPC ya kama man sata

July 11, 2023

Rahotanni daga Najeriya sun yi nuni da cewa kamfanin mai na kasar, NNPC ya gano wani jirgi shake da lita dubu 800 na danyen man fetur da aka sato.

https://p.dw.com/p/4Thss
Hoto: AFOLABI SOTUNDE/REUTERS

NNPC ya gano jirgin ne yayin da yake kan hanyarsa zuwa kasar Kamaru kuma kamfanin ya ce zai lalata man.

Kamfanin ya ce, yana kyautata zaton an sato man ne daga wata rijiyar mai da ke Kudu maso Yammacin jihar Ondo, kana jirgin da aka zuba man na zama mallakin wani kamfani mai suna Holab Maritime Services Limited ne. A bidiyon da NNPC ya wallafa, ya nuna yadda jami'an tsaron Najeriya suka yiwa jirgin man kawanya.

Sai dai har yanzu kamfanin na Holab bai mayar da martani kan zargin ba. Dama dai ana ganin akwai jan aiki a gaban sabon shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu na magance matsalolin da kasar ta shafe shekaru tana fama da su na fasa bututu da kuma satar mai daga rijiyoyin mai a yankin Niger Delta.