1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin gano hanyoyin magance rashin tsaro a Najeriya

February 3, 2020

Tabarbarewar tsaro a Najeriya ta sanya malaman addinai shiga addu'o'i da azumi don rokon Allah Ya kawo karshen ayyukan ta'addanci da sauran ayyuka na ta'asa da ke shafar tattalin arikin kasa da zamantakewar a'lumma.

https://p.dw.com/p/3XDe9
Ko a baya ma an sha taruka don neman kyautata zamantakewar al'umma a Najeriya, kamar nan a wani taro a Kaduna
Ko a baya ma an sha taruka don neman kyautata zamantakewar al'umma a Najeriya, kamar nan a wani taro a KadunaHoto: Katrin Gänsler

Akalla malaman addinin musulunci guda 100 ne kungiyar Islahul Umma Assufiyya ta kasa ta gayyato domin fara azumin kwanaki uku don rokon Allah Ya kawo karshen tashe-tashen hankula da ta'addanci da sauran ayyukan bata-gari da suka addabi al'umma a Najeriya.

Sheikh Salihu Abdullahi Mai-Barota shi ne shugaban kungiyar ta kasa da ya bayyana dalilinsu na shirya wannan taron addu'o'i a Kaduna.

"Sakamakon karuwar tashe-tashen hankula da rashin kwanciyar hankali musamman a arewacin Najeriya ya haifar da koma-baya da hanyoyin dabam-dabam da suka jibanci na bangaren tattalin arzikin kasa, noma da ilmi da harkar kiwon lafiya."

Sheikh Salihu Mai-Barota ya kara da cewa sun gayyato malamai da mahaddata alkurani guda 100 da sauran daga kananan hukumin Kaduna 23 don ganin sun yi wa Najeriya addu'a domin magance fitittinun da ke zama barazana ga zamantakewa tsakanin al'ummar kasa.

Fastor James Wuye da Imam Mohammed Ashafa na kungiyar Interfaith a Kaduna
Fastor James Wuye da Imam Mohammed Ashafa na kungiyar Interfaith a KadunaHoto: picture-alliance/dpa/B. Roessler

Daga cikin batutuwan da aka tattauna wajen taron addu'o'in sun hada da yin kira ga ilahirin 'yan Najeriya na cikin gida da na waje da su dinga yi wa kasar addu'ar neman zaman lafiya. Bugu da kari malaman sun bukaci takwarorinsu Kiristoci su ma su yi wa kasa addu'a.

Malaman sun kuma janyo hankalin sauran masu ruwa da tsaki a kan kara himmatuwa wajen bada tasu gudunmawar wajen fargar da al'umma kan kyautata zamantakewa tsakanin dukkan 'yan kasa.

Idan dai ba a manta ba da yammacin ranar Lahadi kungiyar Kiristocin Najeriya ta CAN a Kaduna ta kammala addu'o'in kwanaki uku tare da azumi don nema wa kasa zaman lafiya da kawo karshen garkuwa da mutane a kasar.

Su a  a nasu bangare kungiyoyin farar hula sun bukaci gwamnati da ta taimaka wa jami'an tsaro da dukkanin kayan aiki na zamani don magance hare-haren 'yan bindiga da masu sata da garkuwa da mutane.