1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin hana satar man fetur a Najeriya

Uwais Abubakar Idris LMJ
September 8, 2023

Majalisar wakilan Najeriya ta fara wani kokari na gano dabarun da za a bi domin shawo kan matsalar satar danyenn man fetur, wanda kasar ta yi asarar sama da Naira tirliyan 16 a cikin shekaru 11 da suka gabata.

https://p.dw.com/p/4W8Fe
Najeriya | Bayelsa | Danyan Man Fetur | Sata
Masu satar danyan man a NAjeriya, na samar da matatar kashin kansu da suke tace shiHoto: Sunday Alamba/AP Photo/picture alliance

Tattalin arzikin Tarayyar Najeriyar dai, ya dogara ne a kan arzikin man fetur din da take da shi. Batun satar danyen man fetur din dai ya sanya majalisar wakilan kafa kwamitin musamman da ya rinka bankado barnar da ake yayin satar danyan man da ke zama tamkar almara ko mafarki. Kwamitin ya gayyaci masu ruwa da tsaki a kan harkar, wadanda suka rinka bayyana irin yadda masu halin bera da rana tsaka ke sace man fetir din Najeriyar suna fita da shi zuwa ketare.

Karin Bayani: Fatan al'umma bayan samun mai a Bauchi da Gombe

Majalisar ta yi wannan kokari ne domin dakile wannan matsala, wacce ke ci gaba da durkusar da tattalin arzikin kasar. Majalisar ta ce Najeriya na asarar kusan kaso 30 cikin 100 na man da take hakowa a kasar ga barayi da ke satarsa, duk kuwa da ci-gaban fasahar zamani ta kula da kare bututun man fetir a kasar. Masu satar dai kan shimfida nasu bututun su nufi wani gefe da shi, inda suke jidar man tamkar babu jami'an tsaro.

Haramtattun matatun fetur a Najeriya

Majalisar ta gayyato kwararren injiniya kana tsohon ma'aikacin hukumar sararin samaniya ta Amurka Dakta Ado Abdu wanda ya kirkiro wata naura da ke amfani da tauraron dan Adam domin shawo kan matsalar, bayan kwashe lokaci mahukunta na watsi da ita domin ya yi mata karin haske. Tun kafin wannan lokaci dai akwai kwamitoci da ke aiki a kan wannan matsala, amma a lokuta da dama bayan irin wannan tonon silili sai kaji shiru.

Karin Bayani: Najeriya: Badakalar cin hanci da rashawa a harkar mai

Satar danyen man fetur a Najeriyar ta sanya kasar gaza hako kason da kungiyar Kasashen masu Arzikin Man Fetur din wato OPEC ta ba ta ikon hakowa, inda daga ganga milyan 200 da dubu 500 da take hakowa kowacce rana a 2005 a yanzu take hako kasa da ganga milyan daya da dubu 77. A yayin da jami'an da ke da alhaki a kan wannan matsala ke mika bayanansu a rubuce ga majalisar, za a sa ido a kan sakamakon da zai biyo baya.