1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamen masu rajin kasar Biafra a Najeriya

Muhammad Bello LMJ
August 14, 2020

Rundunar 'yan sanda a jihar Imo da ke yankin kabilar Igbo, ta ce ta kama 'yan rajin kafa kasar Biafra daga Tarayyar Najeriya su kimanin 100, yayin da suke wani jerin gwanon sake farfado da rajin nasu.

https://p.dw.com/p/3gz6B
NIGERIA Biafra Aba Demonstration
Zanga-zangar masu rajin kafa kasar Biafra a NajeriyaHoto: Getty Images/AFP/P. U. Ekpei

Kungiyoyin rajin kafa kasar Biafra a yankin na Igbo, sun hada da MASSOB karkashin jagorancin Ralp Uwazurike da IPOB ta Nnamdi Kanu da Biafra Zionist Front mai jibi da Isra'ila da wani Benjamin Igwe Onwuka ke jagoranta. Sai dai kuma wacce ta yi kaurin suna wajen zafafa akidar kafa kasar ta Biafra da kuma gwamnatin Najeriya ta kakaba mata tambarin ta'addanci ita ce ta IPOB, wadda daga lokaci zuwa lokaci ta ke fito na fito da jami'an tsaro a yankunnansu na Igbo.

Fito na fiton haramtacciyar kungiyar ta IPOB din dai na baya-bayan nan, ya afku a birnin Owerri na Jihar Imo a yankin. Sun dai yi wani jerin gwano, inda suka tasamma wani guri da wani babban boka yake a garin Orji da suka ce zai ba su maganin bindiga. Ta dai kai ga sun yi arangama da jami'an 'yan sanda, inda aka kama 67 daga ciki.
Wasu bayanan sirri dai da jami'an tsaro a jihar ta Imo da ke zaman cibiyar 'yan rajin Biafran suka ce sun samu shi ne, 'yan rajin na Biafra na kungiyar 'yan ta'addan ta IPOB, na shirya kai farmaki ga jami'an tsaro a jahar tare da nufin wartar makamai daga jami'an tsaron. Sai dai wani mai magana da yawun haramtacciyar kungiyar 'yan rajin Biafran, wani Mr Emma Powerful ya yi kira ga gwamnan jihar Imon, da ya bukaci jami'an tsaron Najeriyar, da su gaggauta sako musu mambobinsu da ake ci gaba da tsarewa a hannun 'yan sanda kafin su kai ga hasala.

Nigeria Biafra | Nnamdi Kanu
Shugaban kungiyar IPOB ta masu rajin kafa kasar Biafra a Najeriya Nnamdi KanuHoto: DW/K. Gänsler

Tun dai bayan yakin basasar Najeriya da yai sanadiyyar salwantar rayukan 'yan kabilar ta Igbo kusan miliyan daya kamar yadda suka sanarwa da duniya,ckabilar ta Igbo ba ta aminta da sakin jiki da zamantakewar tarayya a Najeriyar ba, duk kuwa da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin kabilar ta Igbo da kuma mahukuntan Najeriyar na ci gaba da zama kasa daya al'umma daya. DW dai ta yi kokarin jin ta bakin kwamishinan 'yan sandan jihar Imo, CP  Isaac Akinmoyede kan tashin-tashinar da ta kai ga kamawa tare da tsare masu rajin kafa kasar Biafran, amma hakan ya ci tura.